MDD na son a yi binciken kashe-kashe a Sudan
July 1, 2022Talla
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira ga hukumomin kasar Sudan da su kaddamar da bincike mai zaman kansa, bayan kisan da jami'an tsaron kasar suka aikata a kan masu zanga-zangar neman kawo karshen mulkin soja a kasar.
Cikin wata sanarwar da shugabar hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar, Michelle Bachelet ta fitar musamman kan kisan 'yan Sudan din tara a jiya Alhamis, jami'ar ta nuna damuwa kan abin da 'yan sanda suka yi duk da bayanan da suka yi na cewar ba za su amfani da harsasan gaske ba a kan fararen hula.
Mutum 113 ne dai jami'an suka mutu a Sudan, tun bayan karbe iko da sojoji suka yi a watan Oktobar bara, kuma ya zuwa yanzu babu wani da aka dora wa alhakin kisan fararen hulan.