MDD na son Rasha ta sake tunani kan abinci
July 25, 2023Talla
Antonio Guterres ya ce rashin komawar Rasha ga yarjejeniyar da ta janye daga ciki a farkon wannan wata, zai sanya kasashen da suka dogara da kayan abincin da ke fita daga Ukraine ta wannan tekun cikin yanayi mai muni.
Ya yi wannan kira ne a jawabin da ya gabatar lokacin taro kan lamarin abinci a duniya da aka yi a birnin Rome na kasar Italiya.
Jagoran na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada matsayin kasashen Rasha da Ukraine wadanda a yanzu ke yaki ta fuskar samar da abinci a duniya.
Akasarin hatsi da Ukraine ke fitarwa ta tekun dai na zuwa kasashen Afirka ne da na Gabas ta Tsakiya da ma wasu sassa na wannan duniya.