MDD na son tsawaita wa'adin dakarunta a Kwango
December 20, 2025
Rundunar wanzar da zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke da dakaru fiye da 11,000 a Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwango, na neman tsawaita wa'adin zamansu a kasar har zuwa watan Disambar 2026.
Amurka ta nuna goyon bayanta ga matakin, inda ta bukaci Ruwanda da 'yan tawayen M23 su mutunta yarjejeniyar yankin da aka cimma. Kuri'ar da aka kada na zuwa ne bayan da 'yan tawayen M23 suka kwace iko da manyan garuruwan gabashin Kwango. Amurka dai na zargin Ruwanda da taimaka wa 'yan tawayen, zargin da Ruwandar ta musanta.
Karin bayani: Amurka za ta dauki matakin ladabtar da Ruwanda kan rikicin Kwango
A yayin zaman zauren majalisar Dinkin Duniya, mai wakiltar Amurka, Jennifer Locetta ta ce Ruwanda na M23 na yi wa yarjejeniyar zaman lafiya zagon kasa. A farkon watan Disamba ne, shugabannin Kwango da Ruwanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Washington. Sai dai fadan da aka gabza a yankin Uvira na haifar da fargaba. Kasar Burundi ta ce mutane 85,000 ne suka tsallaka iyaka zuwa kasar domin neman mafaka.