Ana zargin Koriya ta Arewa da sabunta nukiliya
February 9, 2021Talla
Kwararru a harkar makamashi da makaman kare dangi a Majalisar Dinkin Duniya, suna zargin Koriya ta Arewa na cigaba da sarrafa sabbin nau'un makamai masu linzami, tare da neman kayan sarrafa makaman da kimiyyarsu daga saura kasashen duniya.
A 2016 kwamitin sulhu na MDD ta kakabawa Koriya ta Arewa tsauraran takunkumin bayan gwajin makamanta na nukiliyar na farko, inda aka haramta mata fitar da kaya tare da takaita shigo da wasu kayayyakin daga kasashen waje da zimmar tilasta ta rusa tashoshin nukiliyarta.