1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Rikici ya ki cinyewa a Sudan ta Kudu

Mouhamadou Awal Balarabe
March 1, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewa rikicin shugabanci a Sudan ta Kudu ya salwantar da rayukan mutane 440 a watannin karshe na 2021, inda ta ce Riek Machar da Salva Kiir ne suka haddasa shi.

Südsudan Juba - Riek Machar, Salva Kiir
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Patinkin

Wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a wannan Talata( 01.02.2022) ya bayyana cewa akalla fararen hula 440 ne aka kashe tsakanin watan Yuni zuwa Satumban 2021 a yankin Kudu maso yamamcin Sudan ta Kudu, a rikicin da ya barke tsakanin bangarorin kasar da ke rikicin shugabanci.

MDD ta bayyana kungiyar mataimakin shugaban kasar Riek Machar (SSPLM/A-IO) da kuma dakarun Sudan ta Kudu (SSPDF) da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da kuma mayakan sa-kai a matsayin masu hannu wajen cin zarafi al'umma a lokacin wadannan fadace-fadacen siyasa da kuma na kabilanci.  Binciken ya kara da cewa akalla fararen hula 64 ne aka yi wa fyade, ciki har da wata yarinya 'yar shekara 13, yayin da akalla fararen hula 56 suka batar dabo a tsukin wannan lokaci.

Kimanin mutane 80,000 ne dai suka tsere daga gidajensu domin gujewa fada a Sudan ta Kudu kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta.