MDD: Rikicin Sudan ya halaka mutane sama da 500 a wata uku
March 24, 2026
Hare-haren jiragen marasa matuka a Sudan sun halaka mutane sama da 500, a cikin kasa da watanni uku, mafi akasarinsu a jihohi uku na yankin Kordofan, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
Hukumar kare hakkin 'dan adam ta duniya, ta bakin mai magana da yawunta Marta Hurtado, ta shaidawa manema labarai a birnin Geneva cewa sun samu wadannan bayanai ta cikin alkaluma da suka tattara daga ranar 1 ga Janairun bana, zuwa 15 ga Maris.
Karin bayani :Sudan: An kashe gomman mutane a asibiti
Kudancin Kordofan na zama fagen dagar gwabza yakin neman kwatar iko, tsakanin sojojin Sudan da ke karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan, da kuma dakarun RSF masu biyayya ga Muhammad Hamdan Dagalo.
Yakin basasar da ke dab da cika shekaru uku da barkewa, ya yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a, tare da raba wasu miliyan 11 da gidajensu, lamarin da ya janyo halin jin kai mafi muni a duniya, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar.
Karin bayani :Hari daga Sudan ya kashe mutum 18 a Chadi
Ko a wannan Talata, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta tabbatar karin adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai asibitin gabashin Darfur zuwa 70, inda asibitin ya tsaya da aiki.
karin bayani : Hari ya halaka mutane 17 a Sudan
Haka zalika hukumar ta ce adadin wadanda suka jikkata ya kai 146, bayan farmakin da aka ka ranar Juma'a, a asibitin koyarwa na El-Daein, kamar yadda mataimakiyar babban jami'in WHO a Sudan, Hala Khudari ta tabbatar, yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Port Sudan.
Ta kara da cewa mutanen da harin ya halaka da kuma jikkata, sun hada da kananan yara da mata da jami'an lafiya, har ma da masu jinyarsu.