MDD: Sabon takunkumi kan Koriya ta Arewa
December 23, 2017Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sanya sabbin takunkumi a kan Koriya ta Arewa a ranar Jumma'a sakamakon gwajin da take yi a baya-bayan nan na makamai masu linzami masu karfin isa wata nahiya. Wannan sabon takunkumi na da nufin ganin kasar ta tagayyara wajen samun makamashi daga albarkatun man fetir daga wasu kasashe da ma kudaden da kasar ke samu daga ma'aikata 'yan asalin kasar da ke aiki a kasashen ketare.
Matsayar da Majalisar Dinkin Duniya ta cimma za a hana kashi 90 cikin dari na albarkatun na man fetir da ake shiga da shi Koriya ta Arewa inda a yanzu a cikin shekara ganga dubu dari biyar ne za a shigar, sannan an gabatar da shirin mayar da 'yan Koriya ta Arewa da ke aiki a kasashen waje gida cikin watanni 24 sabanin watanni 12 da aka tsara tun da fari.
Amirka da ta gabatar da bukatar ta nemi a shigar da ganga miliyan hudu ne amma da zummar a kara ragewa idan har Koriya ta Arewan ta ci gaba da yin gwaje-gwajen nata na makamin nukiliya.