MDD ta amince da shirin Moroko kan yankin Yammacin Sahara
November 1, 2025
Dubban al'umma sun gudanar da bukukuwan murna a Moroko, bayan da kwamitin sulhu na MDD ya kada kuri'ar amincewa da kudurin da kasar ta gabatar kan shirinta na sakin ragama ga yankin Yammacin Sahara wanda aka shafe shekaru kusan 40 ana takaddama a kansa a tsakanin Rabat da 'yan aware masu samun goyon bayan Aljeriya.
Kwamitin sulhun na MDD ya ba da gayon baya ga wannan shiri da ya bayyana a matsayin mafitar da ta fi dacewa ga yankin da ke karkashin 'yan Polisario wadanda suka dade suna neman a yi kuri'ar raba gardama domin samun 'yancin kai
Shirin na Moroko ya tanadi bai wa yankin 'yancin cin gishin kai kamar sauran yankunan kasar, inda za a samar masa da hukumomi wadanda za ku kasasnce karkashin kasar.
Sarki Mohammed VI na Moroko da bai cika yin jawabi ba ya bayyana wannan mataki a matsayin bude sabon babin tarihi tare kuma da yin jinjina ga shugaban Amurka Donald Trump kan rawar da ya taka wajen warware wannan takaddama ta kusan shekaru 50.
Wannan mataki da aka kai na zuwa ne bayan da Moroko ta yi nasarar samun goyon bayan kasashen yammacin duniya da dama ciki har da Faransa da Spain da Burtaniya kan burinta na mallakar yankin Yammacin Sahara.