MDD ta amince da tsagaita wuta a Siriya
February 24, 2018Talla
Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar goyon bayan tsagaita wuta a Siriya na tsawon kwanaki 30 domin bada damar kai taimakon jin kai ga al'umma.
Da farko dai Rasha wadda ke mara baya ga shugaba Bashar al Asad ta yi barazanar hawa kujerar naki amma daga bisani dukkan wakilan kwamitin sulhun su 15 suka amince da kudirin tsagaita wutar ba tare da wani jinkiri ba.
Kasashen Kuwait da Sweden sune suka gabatar da daftarin kudirin a ranar Laraba yayin da a waje guda shi ma sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kiran dakatar da fada a yankin.
Amincewa da kudirin dai na zuwa ne yayin da jiragen yaki ke luguden bama bamai a gabashin Ghouta gari na karshe dake hannun yan tawaye.