MDD ta bukaci sakin hambarerren shugaban Burkina Faso
February 11, 2022Talla
Yayin wani taron keke-da-keke, kasashe mambobin kwamitin na sulhu su 15 sun yi kiran sojojin na Burkina Faso da su gaggauta sakin hambarerren Shugaba Roch Marc Christian Kabore da ke a hannunsu a yanzu.
Haka ma sun bukaci da a saki sauran jami'an tsohuwar gwamnatin na Burkina da suka kama a ranar 24 ga watan jiya.
Cikin watan Oktoba ne dai Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci mabobin na kwamitin sulhun, da su dauki matakin a kan yawan kwace iko da sojoji ke yi wasu kasashen duniya.
Kwamitin na sulhu wanda ke da cikakken ikon kakaba takunkumai ko daukar matakin soja a kan kasashe, na fama da rarrabuwar kawuna, musamman yadda Amirka da wasu kasashen ke jayayya da Rasha da kuma China.