SiyasaAfirka
MDD ta bukaci yin binciken gaggawa a kan hare-haren Filato
December 28, 2023![](https://static.dw.com/image/63459918_800.webp)
Talla
A cikin wata sanarwa Volker Turk ya bukaci mahukuntan Najeriyada su kafa hukuma mai zaman kanta da za ta gudanar da binciken harin cikin gaggawa, daidai da dokokin kare hakkin bil'adama a duniya, tare da hukunta wadanda ke da hannu.
Kungiyoyin da ke dauke da makamai sun kaddamar da hare-hare tsakanin yammacin ranar Asabar zuwa safiyar Talata a jihar Filato, yankin da ya shafe shekaru da dama yana fama da rikicin addini da na kabilanci.
Yankunan Arewa maso Yamma da tsakiyar Najeriya sun dade suna fama da matsalar ta'addancina 'yan bindiga da ke kai hare-hare a kan kauyuka domin yin fashi da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.