MDD ta ce Myanmar ta gaza kare al'ummarta
October 19, 2017Mahukunta a kasar Myanmar sun gaza wajen bada kariya ga al'ummar Rohingya da ke zama marasa rinjaye a kasar kamar yadda jami'ai da ke nazari kan aikata kisan kiyashi a Majalisar Dinkin Duniya suka nunar.
Mai bada shawara kan harkokin da suka shafi nazarin aikata kisan kiyashi a MDD Adama Dieng da Ivan Simonovic mai bada shawara kan harkokin bada kariya sun bayyana cewa gwamnatin ta Myanmar ta gaza wajen kare Musulman da ke zama saniyar ware a kasar.
Har ila yau cikin jawaban da suka fitar a wannan rana ta Alhamis a birnin na Geneva sun kuma bayyana cewa su ma al'ummomi na kasa da kasa sunki su yi abin ya dace kan wannan al'umma ta Rohingya, ya kuma zama dole su tashi tsaye don su tabbatar da daukar matakai na diflomasiya kan kasar da ta gaza kare rayukan al'ummarta.
Tun dai daga watan Agusta sama da 'yan Rohingya 580,000 suka tsallake daga kasar inda suke neman mafaka a Bangaladash.