1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta ce Zirin Gaza na kara zama kufai

January 6, 2024

Shugaban kula da ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya ce Zirin Gaza na kara zama kufai sakamakon yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.

Shugaban kula da ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths
Shugaban kula da ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin GriffithsHoto: Denis Balibouse/REUTERS

Shugaban kula da ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya ce Zirin Gaza na kara zama kufai sakamakon yakin da ya barke a tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.

Babban jami'in ya ce, yankin ya zama mai hatsari tun bayan fara yakin a ranar 7 ga watan Octoba. Griffiths ya kuma koka kan yadda aka yi asarar dubun dubatan rayuka da yawancinsu mata ne da kananan yara.

Karin bayani: Isra'ila ta ce za a iya shafe 2024 ana yaki a Gaza

A cewarsa, hare-haren da ake kai wa ba kakkautawa kan cibiyoyin kiwon lafiya na haifar da hatsari ga fannin da ma barazanar yunwa. Tuni dai MDD ta bukaci gaggauta kawo karshen yakin tare da yin kira ga bangarorin biyu da ba sa ga maciji da juna da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu karkashin dokokin kasa da kasa.

A share guda, a wannan Asabar din, babban jami'in kula da harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell na ziyara a Labenon yayin da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na ziyara a kasashen Turkiyya da Girka. Dukkannin manyan jami'an na ziyarar ce da nufin tattauna hanyoyin kawo karshen rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya.