1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta dakile shirin kai hari a Hodeiba

Gazali Abdou Tasawa
June 12, 2018

MDD ta dauki matakin hana barkewar wani kazamin fada a wannan Litinin a birnin Hodeiba na Yemen da ke zama babbar tashar jiragen ruwan mai muhimmanci wajen shigar da kayan agaji a kasar da yaki ya daidaita. 

Jemen Hodeida Kämpfer
Hoto: picture-alliance/AP Photo/N. El-Mofty

Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin hana barkewar wani kazamin fada a jiya Litinin a garin Hodeiba na Yemen da ke zama babbar tashar jiragen ruwan da ke da matukar muhimmanci wajen shigar da kayan agaji a kasar wacce yaki ya daidaita. 

Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gana a birnin New York da sabon ministan harakokin waje na kasar ta Yemen bayan da Birtaniya ta sanar da Majalisar Dinkin Duniya kan wani kazamin farmaki da sojojin rindunar kawancan kasashen larabawa da Saudiyya ke jagoranta a yakin na Yemen ke shirin kaddamarwa a birnin na Hodeiba da ke a hannun 'yan tawayen Shi'a na Kungiyar Houthis. 

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani taron gaggawa a asirce inda ya saurari manzon babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Yemen wato Martin Griffiths wanda ke can yana kai gauro ya kai mari tsakanin 'yan tawayen na Houthis da Saudiyya da kuma jamhuriyar Daular Larabawa domin hana kaddamar da wannan farmaki.