MDD ta dauki kudiri kan rikicin Burundi
November 13, 2015Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin da yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da ake ci gaba da fuskanta a kasar Burundi, tare da nuna yuwuwar tura dakarun kiyaye zaman lafiya idan lamarin ya kazance.Kwamitin ya dauki wannan mataki ne a lokacin wani taro na musamman da ya gudanar a wannan Jumma'a
Daukacin mambobi 15 na Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya suka amince da kudirin tare da neman babban sakataren majalisar Ban Ki-moon ya mika rahoto cikin kwanaki 15 kan karfafa dakarun kiyaye zaman lafiya a kasar ta Burundi saboda yadda tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci ke ta'azzara.
Matsayin Faransa kan kudirin MDD kan Burundi
Kasar Faransa ta gabatar da kudirin kuma jakadan kasar da ke Majalisar Dinkin Duniya Francois Delattre ya ce za a yi duk abin da ya dace domin kauce wa makamancin rikicin da ya faru a Ruwanda cikin shekarar 1994 lokacin kisan kare dangin da kusan mutane miliyan daya suka hallaka.
"Wannan kudiri ya kuma tura sako kan kawo karshe tashe-tashen hankula saboda jawabai na kiyayya. Kwamitin Sulhu zai yi abin da ke yuwuwa karkashin ikonsa domin kare kasar ga tsanduma rikici."
Barazanar saka takunkumi ga masu hannu cikin rikicin Burundi
Sannan kudirin na Kwamitin Sulhun ya yi barazanar saka takunkumi kan wadanda suke da hannu cikin tashe-tashen hankula, kana ya nemi ganin an fara tattaunawa domin kawo karshen rikicin.
Matthew Rycroft jakadan Birtaniya na Majalisar Dinkin Duniya ya karanta sanarwar bayan kada kuri'ar:
"Kudirin wanna rana ya zama muhimmin matakin ci gaba na tura sakon hadin kai ga duk bangarorin Burundi kan tattaunawa da kaurace wa kalaman tayar da hankali. Wannan sako ya kara zama mai tasiri daga sanarwar hadin gwiwa na kungiyar kasashen Turai, da Tarayar Afirka gami da Majalisar Dinkin Duniya."
Kimanin mutane 250 suka hallaka tun daga watan Afrilu lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi ya kaddamar da neman wa'adi na uku domin tsawaita mulkinsa. Sai dai masana na ganin duk da tashe-tashen hankula da ake samu zai yi wuya Shugaba Nkurunziza ya ba da kai, saboda akwai wadanda ke take tsarin mulki a Afirka babu abin da ya faru a cewar Antoine Glaser dan jarida kana masanin kasar:
"Da wahala Shugaba Nkurunziza ya mika wuya domin da wahala a rasa kasashe masu irin halin."
Yakin basasa da kasar ta Burundi ta fuskanta daga shekarar 1993 zuwa shekara ta 2005, wanda aka kwashe shekaru 12 tsakanin 'yan tawaye na kabilar Hutu da sojojin gwamnati da tsirarun 'yan Tutsi suka mamaye, lamarin da ya kai ga mutuwar kusan mutane dubu-300. Kuma yanzu ana fargaba saboda kalaman da ake gani suna nuna kiyayya wadanda za su iya sake jefa kasar cikin rikici.