Hasashen rudani a arewa maso gabashin Najeriya
February 16, 2017Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Najeriya na iya shiga rudani a bangaren kyautata al'umura a shiyar arewa maso gabashin kasar, muddin kungiyoyin agaji suka gaza cimma tasiri a cikin watanni 18 da suka rage masu.
Jagoran shirin samar da agaji na MDD a Najeriya Edward Kallon, ya ce da sauran aiki ta fuskar daidaita al'amura a shiyar da ta fuskanci tsananin ta'asar mayakan Boko Haram shekaru 7 da suka gabata.
Jami'in na MDD ya kuma ce ko a bara ma sun fuskanci matsalar karancin kudaden samar da agaji, yayin kuma da a bya-bayan nan, shirin samar da abinci na duniya ya hasaso yiwuwar fuskantar bala'in yunwa.
A halin ma da ake ciki akwai aklla yara kanana dubu 45 da za su iya fuskantar karancin abincin da suke bukata, in har babu tsayeyyen matakin da aka dauka
Sama da mutane dubu 20 ne dai suka salwanta, yayin da wasu miliyan 2 da rabi suka rasa matsugunai sakamakon ayyukan Boko Haram a Najeriya.