Batun sulhu gabanin zaben Burundi
August 23, 2018A cikin wata sanarwa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan halin da ake ciki a kasar ta Burundi, ya nuna rashin jin dadi dangane da yadda bangarorin siyasar kasar ke jan kafa wajen samun matsaya duk da matakin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya dauka na kauracewa zaben mai zuwa.
A cikin sanarwa tasa kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma bayyana fatan ganin an dama da illahirin jam'iyyun siyasar kasar da kuma musamman mata a zaben mai zuwa.
A shekara ta 2015 ne dai Shugaba Nkurunziza ya yi tazarce bayan kammala wa'adin mulkinsa da doka ta masa izini, lamarin da ya jefa kasar a cikin tarzoma da tashin hankali wandanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu 12 a yayin da wasu sama da dubu 40 suka shiga gudun hijira.