MDD ta nuna fargabar samun zabe na gaskiya a kasar Kamaru
September 2, 2025
Majalisar Dinkin Duniya ta fara nuna fargabar yiwuwar gudanar da ingantaccen zabe cikin gaskiya da adalci a kasar Kamaru, a cikin watan Oktoba mai kamawa, sanadiyyar irin kamun ludayin gwamnatin shugaba Paul Biya.
Shugaban hukumar kare hakkin 'dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk, ya koka da yadda ake danne hakkin 'yan adawa, ta hanyar hana su gudanar da gangamin siyasa, har da zargin yunkurin haramta wa wasunsu shiga takara.
Ko a watan Agustan da ya gabata sai da jami'an tsaron kasar suka kama 'yan adawa 53 suka garkame, bisa zargin gudanar da taron siyasa, inji hukumar kare hakkin 'dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya.
Karin bayani:Matasa suna baya-baya da zaben Kamaru
Shugaba Biya mai shekaru 92, na neman tsawaita mulkinsa na tsawon shekaru 43, a zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Oktoban 2025.