SiyasaJamus
MDD ta sake jan hankalin hukumomi a Sudan
December 4, 2021Talla
Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya, Antonio Guterres, shi ne ya nuna wannan bukata cikin wani rahoto da aka mika wa kwamitin sulhun majalisar a jiya Juma'a.
Daruruwan masu fafutukar siyasa da 'yan jarida da wasu da ke tsaye a gefen hanya aka tsare a Sudan, saboda zargin su da hukumomin kasar ke yi na kasancewa masu furjanye wa gwamnati.
Haka nan Majalisar Dinkin Duniyar, ta yi tir da amfani da harsasai masu kisa da jami'an tsaro ke yi a kan masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati, abin da ke ci gaba da haddasa asarar rayuka a kasar.
A ranar 25 ga watan Oktoba ne dai Sudan din ta sake fadawa cikin sabuwar rigimar shugabanci, bayan kwace iko daga hannun firaminista Abdalla Hamdok da jagoran soji Janar Abdel Fattah al-Burhan ya yi.