1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaHong Kong

MDD ta soki daurin da aka yi wa Jimmy Lai

Ahmed Salisu
February 9, 2026

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta soki lamirin Hong Kong kan daurin shekaru 20 a gidan sarka da ta yi wa fitaccen mai sukar China din nan Jimmy Lai.

Hongkong 2014 | Apple Daily | Gründer Jimmy Lai bei Occupy Central
Hoto: Li Huiren

Shugaban hukumar Volker Turk ya ce daurin da aka yi wa Lai ya saba da dokokin kasas da kasa don haka ya zama wajibi mahukuntan Hong Kong su sake shi ba tare da bata lokaci ba. 

Da take tsokaci kan daurin da aka yi wa Jimmy Lai din, Burtaniya cewa ta yi daurin da aka yi masa daidai yake da hukuncin daurin rai da rai duba da shekarunsa.

Ita ma Kungiyar EU sukar daurin na Jimmy Lai na wannan Litinin din ta yi, inda ta ce nemi a sake shi sannan a kyale mutane a kasar su mori 'yancin da suke da shi na fadin albarkacin bakunansu.