1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD ta tsawaita takunkumin hana sayar da makamai a Darfur

Mouhamadou Awal Balarabe
September 12, 2025

Daukacin mambobin MDD sun amince da tsarin tsawaita takunkumin da aka kakaba a 2005 da shekara daya, wanda ya tanadi hana daidaikun mutane biyar tafiye-tafiye, da hana shigo da makamai a yanikin Darfour na Sudan.

Bazuwar makamai na ta'azzara rikici a yankin Darfur na Sudan, a cewar Majalisar Dinkin Duniya
Bazuwar makamai na ta'azzara rikici a yankin Darfur na Sudan, a cewar Majalisar Dinkin DuniyaHoto: picture-alliance/dpa/S. Morrison

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita takunkumin hana sayar da makamai ga yankin Darfur na kasar Sudan da shekara guda. A kuduri da daukacin mambobi suka amince da shi, Majalisar ta tsawaita har zuwa ranar 12 ga Satumba 2026 da tsarin takunkumin da aka kakaba a 2005, wanda ya shafi daidaikun mutane biyar da aka hana tafiye-tafiye, da hana shigo da makamai a Darfour.

Karin bayani: Sudan: Matsalar jin-kai saboda yaki

Jakadan Amurka John Kelley ya ce wannan matakin na aike da sako karara cewar kasashen duniya na ci gaba da jajircewa wajen dakile kwararar makamai da kuma tabbatar da ganin an hukunta wadanda ke da hannu wajen haddasa tashe-tashen hankula a Darfur.

Sai dai a cewar majiyoyin diflomasiyya, wasu kasashe sun nuna dacewar fadada takunkumin hana sayar da makamai zuwa yankin Kordofan, amma kasar Rasha ta nuna adawa da matakin a matsayin mai kujerar na-ki a MDD.

Karin bayani: Sudan: Al'umma na cikin mawuyacin hali

A halin yanzu dai, yaki da ke wakana tsakanin sojoji karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan, da dakarun RSF na tsohon mataimakinsa Janar Mohamed Hamdan Daglo, na lamshe rayukan duban mutane tare da raba miliyoyi da matsugunansu.