Masu sa ido daga MDD za su je Yemen
January 16, 2019Talla
Bayan mako guda da tattaunawar zaman lafiya da aka yi a Sweden a watan da ya gabata, mayakan na Houthi da ke samun goyon baya na kasar Iran da dakarun sojan kasar ta Yemen da ke samun goyon bayan kasar Saudiyya sun zauna inda aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya kan birnin na Hodeidah da ke zama mai muhimmanci kan harkoki na kasuwanci da hanyar samun abinci da kayan agaji ga miliyoyin al'umma a kasar ta Yemen da ke gargara ta fadawa hali na yunwa.
Sakataren MDD Antonio Guterres ya ce masu sa idon su 75 za su sa ido kan yarjejeniyar karkashin aikin da aka kira shi aikin MDD don tallafa wa yarjejeniyar Hodeidah (UNMHA).