MDD ta je tashar makamashin Zaporizhzhya
August 29, 2022Talla
Manyan kasashen duniya sun yi gargadi game da yuwuwar bala'in nukiliya a tashar Zaporizhzhya, inda ake yawan kai hare-hare. Sai dai Kiev da Moscow sun sha musanta kai hari a kan tashar. Sai dai Shugaban Faransa Emmannuel Macron ya ce wajibi a kare tashar. "Wannan yakin ba zai iya gurgunta tsaron nukiliya ba, don haka wannan manufa na na ziyarar kwararru na da mahimmanci, dole a kare wannan tashar makamashin nukiliya tare da tabbatar da kariya ga duk yankin. Ikon Ukrain na mallakar wannan tasha ba za a kalubalance ci ba. Ikon nukiliya bai kamata ya zama wani abu na yaki ba, kuma yana da mahimmanci a kare hakkin Ukrainian a kan wannan tashar makamashi."