1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi gargadi a game da halin da ake ciki a Sudan

October 31, 2025

Sakamakon kashe-kashen da ke faruwa a rikicin kasar Sudan, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan kazancewar lamura a kasar. Lamarin ya kai ga shafar ayyukan jinkai da majalisar ta duniya ke samarwa.

Wasu mata da ke tsere wa rikici a El-Fasher na Sudan
Wasu mata da ke tsere wa rikici a El-Fasher na SudanHoto: AFP/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan halin da ake ciki a Sudan, tana mai cewa tashin hankalin da ke ci gaba a yanzu ya kai kololuwar zalunci kuma na zama babbar barazana ga rayukan jama'a, sakamakon hare-haren da rundunar RSF ke ci gaba da kaiwa.

Rahotanni sun nuna cewa, kwanan nan, birnin El-Fasher da ke yankin Darfur ya fada hannun mayakan RSF, abin da ya jefa al'ummar yankin cikin babban bala'i da tsananin wahala ta fuskar jinkai.

Shugaban harkokin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, Tom Fletcher, ya ce halin da ake ciki a yanzu a Sudan na iya haifar da mummunar masifa ta bil’adama.

Jami'in ya kuma bayyana wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewar ba a Darfur kadai ake samun kashe-kashe ba; akwai ma yawaitar zubar da jini a yankin Kordofan, lamarin da ke hana isar da taimakon jinkai ga dubban fararen hula na Sudan.