MDD ta yi gargadi kan rikicin Kashmir
August 8, 2019Majalisar Dinkin Duniyar ta bukaci kasashen biyu da su kauce wa daukar wani mataki dangane da matsayin yankunan biyu da ake rikici a kansu.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres, ya nuna damuwa kan rahotannin da suka bayyana matsayi da Indiya ta dauka a kan yankin Kashmir.
A cewar Mr. Guterres yin hakan ka iya janyo tabarbarewar yanayi na take hakkin bil adama a yankin.
Tun da fari dai Firaministan Indiya Narendra Modi ya ce an dauki matakin raba yankin Kashmir da kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kai ne saboda raba shi da matsalolin ta'addanci da kuma ci gaba da zama saniyar ware.
A jawabinsa na farko bayan daukar matakin, Firamnista Narendra Modi ya ce gwamnati ta yi wani abin tarihi a shawarar da ta yanke.
Rayuwar miliyoyin al'umar yankin da ya fi rinjayen musulmi a Indiyar, ta shiga garari ne bayan matakin janye matsayi na musamman da suke da shi na kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kan da mahukuntan na Indiya suka yi.