MDD ta yi kira ga bangarori biyu na Libiya
October 12, 2020Talla
Stephanie Williams ta yi wannan kiran ne domin kawo karshen dadadden rikicin kasar da ya janyo asarar rayuka da dama.
Kasar Tunisiya ce za ta karbi bakuncin wannan muhimmin zama tsakanin madugun adawa Khalifa Haftar da kuma bangaren gwamnatin Fayez al-Siraj wanda MDD ta aminta da shi.
Ministan harkokin wajen Tunisiya Othman Jerandi na fatan wannan tattaunawar za ta lalubo da mafita a siyasance ga bangarorin biyu.