1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi kiran a maganta yunwa a duniya

September 24, 2021

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kiran da a samar da daidaito wajen rarraba abinci ga kasashen da ke bukata a duniya.

USA New York | UN-Jahresversammlung | Antonio Guterres
Hoto: Eduardo Munoz-Pool/Getty Images

Mr. Guterres wanda ya yi kiran samar da daidaiton na abinci a lokacin jawabi a kan abin da ya shafi yaki da yunwa lokacin babban taron MDD da ke ci a birnin New York, ya jaddada bukatar wadatuwar abinci mai inganci da kuma amfani ga mutane a koda yaushe.

Akwai dai mutum biliyan uku ba sa samun abinci mai lafiya a duniya, yayin da ake da mutum miliyan 462 da suka yi matukar ramewa saboda rashin koshi.

Ana hakan ne kuwa a cewar Guterres, ake da mutum biyan biyu a duniyar wadanda suke fama da kiba mai tsanani.

Sai kuma karuwar zubar da abinci a cewar sa a wasu yankuna na duniya da ya kai yawan kashi daya cikin uku na abinci da ake da shi a duniya.