1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi shelar neman tamakon kudi

December 5, 2016

Majalisar ta bayyana bukatar taimakon kudi sama da biliyan 22 na dalar Amirka a shekara ta 2017 domin tunkarar matsalolin al'umma a yankunan da ake yaki.

USA UN Sicherheitsrat Generalsekretär Ban Ki-moon über Sanktionen für Nordkorea
Hoto: picture alliance/AP Photo/R. Bajornas


Za ta yi amfani da kudin wajen ayyukan agaji ga mabukata miliyan 92 da dubu 800 a kasashe 33 na duniya a shekara mai zuwa. Jagoran hukumar kula da ayyukan jin kai na MDD Stephen O'Brien ne ya yi wannan shela, a lokacin wani taron manema lbarai da ya kira a wannan Litinin:

"Wannan shi ne yanayi na bukatar taimakon agaji mafi girma da aka taba gani tun bayan yakin duniya na biyu, inda a halin yanzu mutane sama da miliyan 128 ke bukatar taimakon gaggawa domin rayuwa a cikin mutunci"

Wannan dai shi ne adadin kudi mafi yawa da Majalisar Dinkin Duniya ta taba bukata domin tunkarar ayyukan agajin al'ummar duniya mabukata.

Stephen O'Brien ya bayyana cewa sama da kashi 80 daga cikin dari na matsalolin da suka haddasa bukatar, na da nasaba ne da yake-yaken da ake fama da su a kasashen duniya da dama. Kuma kasar Siriya ita ce za ta lakume sama da kashi 50 daga cikin dari na kudaden da take bukata kana kasashen Sudan ta Kudu da na Yemen na bi mata baya.