1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indonesiya: Ba zamu amsa kiran Amurka ba

Zainab Mohammed Abubakar
August 25, 2020

Indonesiya da ke shugabantar kwamitin sulhu na MDD, ta ce ba ta da hurumin ci gaba da daukar mataki kan bukatar Amurka na sake kakabawa Iran takunkumi.

Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Tun a ranar Juma'a ce dai, 13 daga cikin wakilan kwamitin sulhun 15 suka yi adawa da batun, saboda yunkurin na Washington ya sabawa ka'ida, ganin cewar tana amfani da tanadin yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran kan shirin nukiliyarta a 2015, yarjejeniyar da Amurkan ta sa kafa ta shure shekaru biyun da suka shige.

Jakadan Indonesiya a MDD, kuma shugaban kwamitin sulhun na watan Augusta Dian Triansyah Djani, na martani ne kan tambayoyin Rasha da Chaina kan batun a lokacin da ake taro kan yankin Gabas ta Tsakiya.