1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

MDD ta yi watsi da yunkurin soke hukumar agajin Falasdinu

Zainab Mohammed Abubakar
July 12, 2024

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewar, babu wata hukuma da za ta iya maye gurbin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu ta UNRWA.

Antonio Guterres Hoto: Luiz Rampelotto/EuropaNewswire/picture alliance

Kasashe 118 sun goyi bayan kungiyar agajin a matsayin wadda ta zama wajibi, a daidai lokacin da Isra'ila ke kara kaimi na bukatar a wargaza ta.

Hukumar ba da agajin ta Majalisar Dinkin Duniya tana ba da ilimi, kiwon lafiya da taimako ga miliyoyin Falasdinawa a zirin Gaza, da Yammacin Gabar Kogin Jordan, da Siriya da kuma Lebanon. Tun bayan da yaki ya barke watanni tara da suka gabata tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinawa a Gaza, jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun jaddada cewar UNRWA ce kashin bayan ayyukan agaji.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana kira da a wargaza hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta Falasdinu, yana zarginta da tunzura mutane kyamar Isra'ila, kuma a halin yanzu majalisar dokokin Isra'ila tana nazari ayyana UNRWA a matsayin kungiyar ta'addanci.

Tuni dai kasashe da dama suka dakatar da kudaden agaji wa hukumar ta MDD, saboda zargin da Isra'ila ta ke yi na cewar, wasu jami'anta na da hannu a harin ba-zata na Hamas a ranar 7 ga watan Oktoban bara, harin da ya janyo yakin da Isra'ilan ke yi a Gaza a yanzu.