1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Sojoji na sayar wa 'yan tawaye makamai a Afirka

February 15, 2023

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da safarar miyagun kwayoyi da dakile aikata laifuka ya ce galibin makaman da ke yawo a kasashen Sahel na fitowa ne daga cikin nahiyar Afirka.

Hoto: Camille Laffont/AFP/Getty Images

A yayin da yake kaddamar da wani sabon rahoto a kan matsalar yaduwar makamai a Afirka, babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da aikata laifuka, Francois Patuel, ya ce duk da cewa akwai hujjojin da ke nuna ana shigo da makamai daga Faransa da kuma Turkiyya zuwa Najeriya, amma bincikensu ya nuna cewa akasarin makaman da ke hannun kungiyoyi da dedekun jama'a ba bisa ka'ida ba, na fitowa ne ko dai ta hanyar cin nasara kan jami'an tsaro a fagen daga ko kuma ta hanyar sayar da makaman da wasu sojoji marasa kishi kan yi.

MDD ta ce safarar makamai zuwa ketare a kasar Libya ta ragu sosai a cikin shekaru 10 da suka gabata. Sai dai majalisar ta ce kasashen Saliyo da Laberiya na zama wasu karin kasashen da makamansu ke yawo a hannun mayaka a kasashen Sahel. Tuni dai majalisar ta bukaci gwamnatocin kasashen da su kara kaimi domin shawo kan wannan matsalar.