1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

MDD: Tallafin jin kai a Siriya

March 31, 2021

Kungiyar Tarayyar Turai da sauran manyan kasashen duniya da ke bayar da tallafi sun cimma matsayar bayar da tallafin kimanin dala biliyan shida a matsayin taimako ga Siriya.

Belgien Brüssel | Pressekonferenz Internationale Geberkonferenz Syrien
Hoto: Dursun Aydemir/AA/picture alliance

Alkawarin bayar da tallafin zunzurutun kudin na zuwa ne bayan kammala taro tsakanin Majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar Tarayyar Turai, inda Majalisar dinkin duniya ta yi fatan cimma matsayar hada dala biliyan goma.

Da tabbatar da alkawarin, Kwamishinan gudanar na EU Janez Lenarcic ya ce ba ya ga tallafin, cibiyoyin kudi da masu bayar da gudumawar sun bayar da rancen kudi har dala biliyan bakwai.

A cewar rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, fiye da rabin al'ummar kasar Siriya ne suke tsananin buktar tallafi yayin da aikin jin kai ke fuskantar tasgaro saboda annobar coronavirus. Kimanin mutane miliyan daya da rabi ne suka rasa rayukansu yayin da da dama ke gudun hijira a kasahen makwafta kawo yanzu tun bayan barkewar yakin basasa shekaru 10 da suka gabata a kasar.