1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Wasu mutum miliyan 1 za su tserewa Sudan

June 28, 2023

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nunar da cewa wasu karin mutane fiye da miliyan daya ne za su sake tsere wa rikicin Sudan nan da watan Octoban wannan shekarar.

Masu tserewa rikicin Sudan
Hoto: AFP

Kawo yanzu dai kimanin mutane 600,000 ne suka tsere wa kasar zuwa kasashen Masar da Chadi da Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Mataimakin kwamishnan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, Raouf Mazou ya ce sun yi kiyasin ne saboda yadda abubuwa ke tafiya a Sudan, yayin da rikici tsakanin shugaban dakarun sojin kasar Abdel-Fattah Burhan  da kuma shugaban mayakan RSF Mohammed Hamdan Dagalo ke shiga mako na 10.

Ko da yake bangarorin biyu da ba sa ga maciji da juna sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta albarkacin bukukuwan babbar salla da al'umma musulman duniya ke gudanarwa.