SiyasaAfirka
MDD: Mutane miliyan 29 na neman agaji a kasashen Sahel
April 28, 2021Talla
Daraktan Yanki na Shirin Samar da Abinci na MDD Chris Nikoi a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce a kasashen Burkina Faso da arewacin Kamaru da Chadi da Mali da Nijar da kuma arewa maso gabashin Najeriya akwai karin sabbin mutane miliyan biyar da ke bukatar agaji idan an kwantata da shekarar da ta gabata.
MDD ta ce yawaitar tashin farashin kayan abinci da rashin tsaro ke haddasawa a kasashen Sahel din na haifar da matsananciyar yunwa da karancin abinci a tsakanin al'umma, tana mai gargadin cewa mutane miliyan 29 da ke bukatar agajin ba wai a rubuce kawai suke ba, suna nan a zahiri kuma suna rayuwa cikin kunci.