SiyasaAsiya
MDD za ta janye dakarunta da ke iyakar Lebanon da Isra'ila
February 10, 2026
Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta janye dakarunta na wanzar da zaman lafiya da ke aiki a Lebanon wato UNIFIL, a tsakiyar shekarar 2027 mai zuwa.
Rundunar wadda aka kafa a shekarar 1978, ta gudanar da aikinta a kan iyakar Lebanon da Isra'ila, sannan kuma a baya bayan nan ta yi aiki da rundunar sojin Lebanon, wajen kwance damarar kungiyar Hezbollah, biyo bayan gwabza fada da sojojin Isra'ila.
Karin bayani : Isra'ila ta kai sabbin hare-hare Lebanon
Mai magana da yawun rundunar Kandice Ardiel, ta ce bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hezbollah da Isra'ila, a watan Nuwamban 2024, an rage dakaru 2,000 daga cikin tawagar, wadda yanzu haka ke da dakaru 7,500 daga kasashe 48 na duniya.