MDD za ta rage yawan sojojinta da ke Darfur
March 11, 2015Za'a yi garon bawul tare da rage yawan rundunar sojin kiyaye zaman lafiya mafi girma a duniya, sakamakon gazawarta na kare rayukan fararen hula da ke Darfur, lardin Sudan mafi girma da 'yan bidiga ke cigaba da cin karensu babu babbaka.
A daidai lokacin da jami'an diplomasiyya da na MDD ke ganin cewar rage yawan dakarun zai yi tasiri wajen samar da tsaro, masu lra da al'amura na dasa ayar tambaya dangane da makomar miliyoyin al'ummar lardin da suka yi shekaru 12 suna tsakiyar wannan rikici da ya haddasa asarar rayuka.
Tun a shekara ta 2003 ne dai rikicin Darfur ya barke, lokacin da Larabawa bakaken fatar lardin suka dauki makamai domin yakar gwamnatin Khartum da ke karkashin Larabawa farararen fata, kan zargin da suka yi na nuna musu wariyar launin fata. Duk da cewar an samu raguwar yawan kashe kashen mutane da aka yi a 'yan shekarun baya bayannan, mahara na ci gaba da addabar mutane, a yayin da dakarun gwamnati ke ci gaba da kai hari kan kungiyoyin tawaye.