MDD za ta rufe sansanin 'yan gudun hijirar Dzaleka a Malawi
July 10, 2025
Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta sanar da cewa za ta takaita ayyukanta a sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a Malawi wanda ke dauke da mutane sama da dubu 57,000 daga kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda da Somaliya da Burundi da kuma Habasha.
Karin bayani:'Yan Mozambik na guduwa zuwa kasar Malawi
Sansanin 'yan gudun hijirar na Malawi wato Dzalekana cikin wadi na tsaka mai wuya, sakamakon dakatar da tallafi da kungiyoyin kasa da kasa da dama suka yi har ma da dakatar da shirin horas da al'umma dabarun dogaro da kai.
Karin bayani:Annoba ta halaka mutane 214 a Malawi
Kungiyoyin fararen hula sun nuna damuwarsu kan yadda za a ci gaba da samar da ababan more rayuwa da na sauran bukatun yau da kullum a sansannin 'yan gudun hijirar na Dzaleka musamman ga mata da kananan yara.