1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me sauya shekar gwamnan Kano zuwa APC ke nufi?

Zainab Mohammed Abubakar
December 29, 2025

Masana da ‘yan siyasa sun bude shafin martini kan yunkurin komawar gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf zuwa jamiyyar APC daga jam'iyyar NNPP.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir YusufHoto: Nasiru Salisu Zango

An dade dai ana yada jita jitar wannan batu amma fitowar wasu na hannun daman gwamna Abba suna masu yin kira da a koma APC yasa mutane sun gamsu cewar hakika gwamnatin Kano ta gama tattara komatsai domin komawa APC sai dai sanarwar rashin goyon tafiyar da aka jiyo daga bakin shugaban NNPP na Kano ya tabbatar da cewar ba da yawun madugun darikar Kwankwasiyya ake shirin hijirar ba.

Tsohon gwamnan Kano, Engr. Rabiu'u Musa KwankwasoHoto: Nasiru Salisu Zango

Ga dukkan alamu dai a iya cewar zaman ya kare, ma'ana dai gwamnatin Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta katse auran ta da jamiyyar NNPP tare da shirin karbar sadaki domin kulla sabon aure da jamiyyar APC me mulkin kasar, koda yake an dade ana kiran madugun darikar Kwankwasiyya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso kan ya karbi wulayar shiga APC domin samun sassaucin adawa da barazanar tankwabe nasara koda an same ta, amma kememe ya ce ba abin dauka ba domin bazai shiga tafiyar da babu sharudda da gwababan kai'idoji ba.

To amma sanarwar wasu jiga jigan fadar gwamnatin Kano, da sanarwar Litinin din nan da aka jiyo daga bakin mai magana da yawun kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta ALGON sun nuna cewar daki ba zai tashi ragaya ta zauna ba, Suraj Imam Dala shi ne kakakin kungiyar ya ce yau babu zama domin su suna kan kira da lallai Kwankwaso da Abba su dauke su, su kai su jamiyyar APC.

Sai dai ga alama an sami farraku, domin kungiyar daliban da gwamnatin Kwankwaso ta kai karatu kasashen ketare ta bakin shugaban ta Dr. Mansur Hassan Kumbotso su kam suna nan daram a NNPP,  kuma wulayar su na tare da Madugu Kwankwaso.

Gwamnan Kano, Abba Kabir tare da Rabi'u KwankwasoHoto: Nasiru Salisu Zango

Da safiyar Litinin din nan dai aka jiyo shugaban jamiyyar NNPP a Kano Hashimu Suleiman Dungurawa na cewar suna da masaniyar wannan yunkuri amma suna rokon masu yi su kiyayi kaurace wa NNPP.

Tuni dai jamiyyar APC ta bakin sakatarenta na Kano Ibrahim Zakari Sarina ta bayyana cewar suna maraba da bakin amma fa ko an shigo sai an zauna gemu da gemu. To ko me wannan guguwa ke nufi ga makomar darikar Kwankwaiyya Dr. Said Ahmad Dukawa da ke zama masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Bayero ta Kano, ya ce shi a zatonsa wannan tsari shiri ne kawai tsakanin kwankwaso da Abba. Tuni dai wannan batu ya zama wani babban maudu'in tattaunawa a Kano da kewaye.