1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Me ya sa ake son Rasha a yammacin Afirka?

Usman Shehu Usman
August 18, 2023

Die Zeit ayar tambaya ta aza, ta ce me ke kawo kaunar Rasha a kasashen yammacin Afirka. Jaridar ta ce watakila talauci da rashin hangen wata makoma a tsarin da ake da shi yanzu su ne ke sa Rasha ke samun tasiri

Nach dem Militärputsch im Niger - Protest im Stadion
Hoto: AFP

Irin yadda Faransa ke ci gaba da juya al'amura a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka ya sa yanzu kasashen ke neman sabbin kawaye. Jaridar ta ce babban misali yadda aka ga magoya bayan soji a Nijar da ke zanga-zangar nuna goyon baya tare da daga tutar Rasha suna kuma kona tutar Faransa. Hakan ba komai ba ne illa nuna cewa sun gaji da mulkin mallakar Faransa suna neman sabbin kawaye. Kama daga shekara ta 2020 yanzu a yankin Sahel wanda duka rainon Faransa ne ba abin da ake gani sai juyin mulki, kama da Mali, Chadi, Burkina Faso da kasar Guinea, duk a yanzu sojoji ne ke mulkin kasashen.

Duk wadannan yankuna da ke samun tashe tashen hankula suna aza ayar tambaya, wai shin za mu ci gaba da dasawa da turawan mulkin mallaka ko kuma za mu nemi sabbin kawaye kamar Rasha ko China? A yanzu dai abinda ake gani a fili shi ne kasashen na neman komawa kawance da Rasha.

Nijar, Yamai | Zanga zangar matasa kan takunkumin ECOWASHoto: Balima Boureima/REUTERS

A sharhinta jaridar Süddeutscher Zeitung, ta duba yankin na Afirka ne mai fama da tashin hankali. Inda ta fara da kasar Sudan ta na mai cewa tsawon watanni hudu, tsoffin janar-janar guda biyu ke fafatawa don dare karagar mulki a Sudan, ba tare da la'akari da asarar da aka yi ba.

Yayinda can nisan kilomita 4,000 a yammacin Sudan, a yankin Sahel, ana fafatawa da 'yan ta'adda masu ikrarin jihadi. Tun bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar, wata kasa da ta fada hannun sojoji. Rikicin na iya dagula zaman lafiyar yankin baki daya. Inda lamarin ke rikidewa.

Niger, Yamai | Masu zanga zanga dauke da tutar RashaHoto: Sam Mednick/AP/dpa/picture alliance

Frankfurter Allgermeine Zeitung shrahinta kan sabon rikicin kasar Libiya ne, inda ta ce alhakin karuwar tashe-tashen hankula a babban birnin kasar Tripoli a wannan makon shi ne rugujewar da ke bayyana halin da ake ciki a Libya. Jaridar ta ci gaba da cewa hayaki  ya turnuke sararin samaniyar Tripoli a farkon mako. 

Tashin gobara a kan tituna, farar hula cikin fargaba, an rufe filin jiragen sama al'amuran irin wannan an dade ba su faru ba a Tripoli tsawon lokaci. Sai dai a farkon mako, fafatawa tsakanin 'yan bindiga biyu masu karfi ta kara ruruwa. Wannan dai shi ne fada mafi muni da aka shafe tsawon watanni ana gwabzawa a babban birnin kasar Libya, kuma barkewar tashin hankalin ba wai kawai tunatarwa ce ga mazauna kasar ba cewa kasar na cikin wata makarkashiya ta kungiyoyi masu dauke da makamai, amma abu ne da ke nuna cewa zaman lafiya a Libiya da sauran jan aiki a gaba.