Me ya sa ake tilasta wa yara aikin da ya fi karfinsu?
June 12, 2025
Yau Alhamis, 12 ga watan Yuni, rana ce da MDD ta ware domin yaki da ayyukan yara.
A wannan shekara, ranar ta mayar da hankali ne kan wani muhimmin ci gaba da aka samu kawo yanzu a fanin yaki da ayyukan yaran da shekarunsu ba su kai ba.
A farkon shekara ta 2020, kashi daya cikin 10 na yara masu shekaru biyar zuwa sama na yin aikin da ya fi karfinsu saboda shekarunsu ba su kai ba. Abin da aka kiesta cewar ya kai kimanin yara miliyan 160, ciki har da 'yan mata miliyan 63 da maza miliyan 97 da suka kasance a cikin wannan hali a duniya.
A cewar Asusun yara na MDD UNICEF, yaron da ke kasa da shekaru 14 bai kamata ya yi aiki ba, ya kamata a ce ya kasance a makaranta a wannan lokaci. Afirka ita ce ta farko a cikin yankunan, a cikin kashi ɗaya cikin 100 na yara masu yin aiki, yayin da Asiya da Pacific suna a matsayi na biyu.
A Madagaska da Guinea da Saliyo da Togo an kara samun yara da ke yin aiki a cikin gonaki na kada ko doya da sauransu.Clement yaro ne dan kimanin shekaru 12 dake aikin kwasar kasa a Togo.
"Ina a aji na biyar na firamare, ina yin aiki daga karfe 12 na rana har zuwa karfe biyar na yamma, ba a bani kudin aikin da na yi, kawuna ke zuwa ya karba ya raba kashi biyu ya bani daya, ciki na kan sayi takalmi shikenan".
Tun daga shekara ta 2000, duniya ta ci gaba da samun ci gaba wajen rage aikin yara. Amma a cikin 'yan shekarun nan, rikice-rikice, da cutar SIDA sun jefa iyalai da yawa cikin talauci kuma sun tilasta wa ƙarin miliyoyin yara yin aiki. Sawadogo Musa na daya daga cikin kungiyoyin agaji da ke shugabantar wata kungiyar agaji a Mali da ake kira Cadest, ya ce ciwo maganinsa ake nema.
"Daya daga cikin abubuwan da ke janyo a saka yara aiki wadanda shekarunsu ba su kai ba shi ne, talauci muna tamaika wa iyaye ta hanyoyin samun 'yan kudade domin su rika daukar mayan wadanda za su rika yin ayyukan".
Kungiyar Kwadago ta kasa da kasa (ILO) ta yi kira da a tabbatar da cikakkiyar yarjejeniya mai lamba 138 , wadda ta kayyade shekaru 15 na yara kafin soma yin aiki.