1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar samar da masarautu a jihar Adamawa

Abdul-raheem Hassan M. Ahiwa
December 17, 2024

Wata dokar da gwamnatin Adamawa ta samar a ranar Litinin 16 ga watan Disambar 2024, ta tabbatar da Lamidon Adamawa Dr. Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar a hukumance.

Nigeria | Umaru Fintiri Lamido Adamawa
Hoto: Abdulraheem Hassan/Domiya Terry/DW

Ana iya cewa, wannan shi ne karo na farko da batun kafa sabbin masarautu ya dauki hankali a tarihin jihar Adamawa da ke arewacin Najeriya, tun bayan kafa jihar daga rusasshiyar jihar Gongola yau shekaru 33 da suka shude. Wannan mataki ya cire shakku a zukatan wasu al'ummar jihar da ke zargin gwamnati da sanya siyasa a yunkurin rage tasirin masarautar Adamawa mai dadadden tarihi.

Me ya faru kafin samar da sabuwar dokar?

A ranar 4 ga watan Disamba na shekarar 2024, Gwamna Fintiri ya sanya hannu a kan wata doka ta daban mai kama da wannan, wacce ta ba shi ikon ƙirƙirar sabbin gundumomi 84. Bayan nan gwamnan, ya aika wa majalisar dokokin jihar wasika ta neman izinin amincewa da kudirin nadi da kuma tube wa sarakuna rawaninsu a jihar. Cikin gaggawa kuma kudirin ya samu tsallake karatun farko da na biyu.

Wannan na zuwa ne bayan salon da aka gani a wasu jihohin arewacin Najeriya, inda gwamnoni ke sauya dokokin da suka shafi masarautu domin ƙirƙirowa ko soke masarautun, wani abu da ake ganin yana rage ƙarfin gidajen sarauta da ke da daɗaɗɗen tarihi.

Me sabuwar dokar ke nufi?

Idan gwamna ya bayyana kananan hukumomin da za a girka a sabbin masaratun gudu uku da ya kirkiro, shugabanin masarautun zai rika zagayawa tsakanin sabbin sarakunan jihar masu daraja ta daya.

Ma'aikatar kananan hukumomin ce za ta rika biyan albashin sarakunan gargajiyan kai-tseye daga asusun gwamnatin jiha, a maimakon kananan hukumomi da ake yi tsawon shekaru.

Me ya sa kirkiro da sabbin masarautu a Arewa ke da alaka da siyasa?

Masarautu masu dumbin tarihi da daraja a arewacin Najeriya, sun shiga rudani a baya-bayan nan sakamakon matakan da majalisun dokokin jihohin kasar ke dauka na yi wa dokokin da suka samar da su kwaskwarima.

Majalisar dokokin jihar Kano alal misali, ta amince da dokar gyaran masarautun jihar a watan Mayun wannan shekara da muke ban kwana da ita ta 2024, inda gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya mayar da Sarki Muhammadu Sanusi na II kan karaga a matsayin Sarkin Kano, bayan sauke shi da tsohon gwamnan jihar Dr. Abudullahi Umar Ganduje ya yi a shekarar 2021, matakin da ya jefa jihar cikin rudani da jigilar zuwa kotuna a matakai daban-daban, inda kallo ya koma sama, a kokarin neman sahihin hukuncin da zai tabbatar da ko waye sarkin Kano, tsakanin Sarki Sanusi da kuma Sarki Aminu Ado Bayero. Batun da har yanzu aka gaza kai ga karshen shari'o'in.

A jihar Adamawa, wasu na danganta lamarin da siyasa saboda kalaman da ake zargin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya yi a lokacin gangamin yakin neman zabe a shekara ta 2019 cewa "za mu fasa kwarya"

Hoto: Abdulraheem Hassan/Domiya Terry/DW

A shekarar 2016, Lamidon Adamawa Dr. Muhammdu Barkindo Aliyu Mustapha ya soke sarautar tsohon gwamnan jihar Murtala Hammanyero Nyako a matsayin Sarki Yamma Adamawa, tare da korar sa a majalisar masarautar, abin da wasu ke ganin tarihi ne ya maimaita kansa a jihar. "Shi ke nan siyasa ta bata harkar sarautar gargajiya a Arewa" a cewar Isuhun Dila Paki wani mai bibiyar lamuran siyasa da harkokin yau da kullum a shafukan sada zumunta daga jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Abin da jama'a ke cewa kan sabuwar dokar

Tun bayan da gwamnati ta mika wa majalisar bukatar samar da dokar sabbin gundumomi da masarautu a jihar Adamawa, ana ta samun mabanbantan ra'ayi kan dacewar yunkurin da kuma akasin haka.

"A gaskiya bani da matsala da karin masarautu, domin al'umma sun yi yawa. Kuma masarautun yanzun, na ado ne ba su da ikon kasa, rage wa srakuna aiki zai fi."  Inji Ahmad Garba daga jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Mas'ud Muhammad Mk daga Potiskum a jihar Yobe a arewa maso gabashin Naajeriya ya ce, "Kullu dai jiya i yau babu wani abun kirki a Arewa sai maganar sarauta. Duniya na ci gaba da bunkasa ta hanyar gina kasa Arewa na ta rigima kan sarauta."

Sakin Kano, Muhammadu Sanusi IIHoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Bisa al'ada, ana ganin masarautun gargajiya  a mastayin wani jigo a cikin al'ummar yankin Arewa, sai dai wasu na ganin darajar masarautun sun fara gushewa saboda siyasa. "A yadda ake tafiya yanzu, duk wanda ke mulkin siyasa, shi ne ke da masarautu. Sarakuna ba su da ikon adawa da gwamnati saboda kare rawaninsu." In ji wani jigo a gwamnatin Najeriya da bai so a bayyana sunansa. Ya kuma kara da cewa "Dole su (Sarakunan) su nuna wa gwamnatocin suna tare da su."  don haka, "An mayar da sarakunan gargajiya karen farautar jam'iyyun siyasa" in ji shi.

A nata bangaren gwamnatin jihar Adamawa ta ce matakin kirkirar sabbin masarautun da gundumomi, ya biyo bayan bukatun da al'umma suka nuna ne na a yi hakan. "Maimakon a duba yadda za a hada masaratun da suke tare a tarihi, amma sai ga shi ana kirkiro da masarautun je ka na yi ka wanda yake rage darajar masarautun.." a cewar wani dan jihar Adamawa.

Lamidon Adamawa da Gwamna Umaru FintiriHoto: Abdulraheem Hassan/Domiya Terry/DW

A kundi na 18 kashi na biyu na sabuwar dokar tsarin sarauta ta shiyya na cewa "Za a samar da shugabanci a kowane bangare na Adamawa, wato yankin tsakiya da Kudu da kuma arewacin jihar wanda a nan ne kadai za a rika bin tsarin shugabanci na karba-karba." kamar yadda Musa Mahmoud Kallamu, shugaban kwamitin watsa labarai a majalisar dokokin jihar Adamawa ya yi wa manema labarai karin bayani a ranar 13 ga watan Disamban 2024. Ya kara da cewa "Amma dukkansu za su rika bayar da ba'asi ga mar girma Lamidon Adamawa Dr. Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, in ji shi.

Da yake tsokaci kan zargin sabuwar dokar na da nufin rage wa Wazirin Adamawa Alh. Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban Najeriya matsayi a masarauta, Dr. John Gamsa tsohon kwamishinan jihar Adamawa kuma mai taimaka wa gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri kan harkokin yada labarai ya ce "Akwai rashin fahimta kan abin da sabuwar dokar ta kunsa, da kuma son kirkiro abin da ba shi ne ba"