Najeriya: Me ya sa jihohi zargin tarayya?
February 2, 2026
Tun daga farkon watan Nuwamba ne dai, aka fara rikicin kudi, inda jihohin suka sa kafa su shure kudin da Abujar take fadin ta ba su. An dai kare watan Janairun da ya gabata ba tare da mafi yawan jihohin sun iya biyan albashin ma'aikata ba, sakamakon rikicin da ke dada kamari cikin kasar a halin yanzu. Jihohin sun fara nunin yatsa kan tarayyar da suke zargi da tara triliyan kusan hudu cikin watan Nuwambar bara, amma kuma aka kare da rabon kasa da rabin kudin a matakan kasar guda uku. Rikicin kuma da ya dora ya zuwa Janairun bana, inda gwamnonin suka sa kafa sukai uwar watsi da triliyan daya da miliyan dubu dari tara da Abujar ta ayyana ba su.
Korafin gwamnonin dai na zaman kokari na karkatar da kudin tarayyar a bangaren na Abujar, domin biyan bukatun son rai. A yayin kuma da Abujar take fadin ta yi uwa da makarbiya, wajen ceto jihohin daga rushewa. Kimanin jihohi 27 ne dai ba sa iya biyan albashi kafin hawan Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan madafun iko, a fadar ministan yada labarai na kasar. Matakan farfado da tattalin arzikin da Abujar ta kirkiro ne suka kai ga sauyin lamura, a jihohin da yanzu haka ke neman mantawa da talauci a fadar Abdul Aziz Abdula Aziz da ke zaman kakakin gwamnatin kasar.
Koma ya take shirin da ta kaya a tsakani na jihohin da ke ta korafin an kwashe da Abujar da ke fadin an sauya, daga dukkan alamu sabon sauyin da ke cikin jihohin kasar na gaza tasiri ga rayuwa da makoma. Duk da cewar jihohin na biyan kudin fanshon tsofaffin ma'aikata da dama, sun kau da kai ga rayuwa da makomar al'ummar jihohin kasar da daman gaske. Ibrahim Jibo dai na zaman tsohon kwamishinan tsara tattalin arziki a Zamfara da kuma yake fadin da sauran tafiya, a tsakanin yawan kudin da ma tasirinsa ga al'umma.
Sauyi ga rayuwar al'umma ko kuma riba a cikin aljihun masu mulki na kasa, a cikin neman inganta rayuwa da makoma ne dai Abujar ta zare tallafin man fetur ko bayan jeri na haraji iri-iri. Matakin kuma daga dukkan alamu ya kwashe kudi a hannun talaka ya mai da su zuwa lalitar 'yan mulki, ana shirin fuskantar zabe tare da karuwar talaucin da ya haura kaso 60 cikin 100 da doriya duk da matakan sake farfado da tattalin arziki cikin kasar. Jihohin arewacin Tarayyar Najeriyar sun samu karuwar da ta kai kusan kaso 150 cikin 100 na kudin tarayyar, a shekaru biyu na gwamnatin ta Tinubu ko bayan yawan kudin kananan hukumomin da gwamnoni na jihohin ke sarrafa su har ya zuwa yanzu.