Me ya sa Merkel ke takara karo na hudu?
September 21, 2017A nan DW mun samu tambayoyi masu yawa daga masu saurare, kan me ya sa har yanzu Angela Merkel ke son tsayawa takara? To Hausawa na cewa waka a bakin mai ita tafi dadi, don haka DW muka tambayi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel shin me ya sa take takara a karo na hudu? Sai ta ce akwai bambancin tsarin tsakanin kasa izuwa kasa. Misali akwai masu tsarin zaban shugaban kasa kai tsaye, kamar na Amirka da Faransa, wato kamar yadda yake a kasashen Najeriya da Nijar da Ghana, inda shugaban kasa zai yi wa'adi biyu kawai kuma ba halin yin ta-zarce. Angela Merkel sai ta kara da cewa
"To a nan Jamus jam'iyyu ake zaba ba shugaban kasa ko shugaban gwamnati ba. Don haka ba zan takaita wa'adi ga jam'iyya ba. To kuma daga cikin jam'iyyun ne suke zaban daya a cikinsu wanda zai zama shi ne jagoran 'yan takara. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba'a kayyade wa'adin mulki ba. Amma misali a nan Jamus ma ai an kayyade wa'adin kujerar shugaban kasa, wato zai yi sau biyu kacal kuma ba ta-zarce, sabanin na shugaban gwamnatin"