1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSaudiyya

Abu Dhabi: Ina makomar alaka da Riyadh?

May 1, 2026

Ficewar Hadaddiyar Daular Larabawa daga kungiyar Kasashen masu Arzikin Man Fetur ta Duniya OPEC, na nuna wani sauyi a fannin siyasa da kuma aika sako mai muhimmanci ga Saudiyya.

Hadaddiyar Daular Larabawa | OPEC | Fita | Saudiyya | Dangantaka | Iran
Kungiyar Kasashe masu Arzikin Man Fetur a Duniya OPECHoto: Barbara Gindl/dpa/picture alliance

Manazarta da kwararru a harkar makamashi na ci gaba da muhawara kan shawarar Hadaddiyar Daular Larabawa ta ficewa daga kungiyar kasashen Kasashen masu Arzikin Man Fetur ta Duniya OPEC da kuma kawancen OPEC+. Ministan makamashi na kasar Suhail al-Mazrouei a shafinsa na X ya bayyana cewa, matakin na matsayin juyin-juya hali a harkar mai da ya yi daidai da manufofin da suka dace a harkar kasuwancin mai na tsawon lokaci.

Cimma muradu ko mayar da martani?

Ya kara da cewa, lokaci ya yi da za su mayar da hankali kan abin da muradun kasarsu ya tanada da kuma jajircewa ga masu zuba jari da abokan huldar cinikayya a kasuwannin makamashi na duniya. A cewar kamfanin dillancin labarai na Hadaddiyar Daular Larabawan WAM, halin da Tekun Fasha da kuma Mashigar Hormuz suka shiga ne ya janyo yanke wannan shawara. A matsayin wani bangare na yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kan Iran, Tehran ta kai hari kan Abu Dhabi da dubban jirage marasa matuka da makamai masu linzami.

Hare-haren Iran sun yi barna mai yawa a Hadaddiyar Daular LarabawaHoto: REUTERS

Hare-haren sun lalata kayayyakin more rayuwa da wuraren samar da mai, baya ga sansanonin sojan Amurka da ke kasar. Kiran da Abu Dhabi ta yi na kasashen yankin Gulf su dauki matakin hadin gwiwa na soja su sake bude Hormuz da ke zama wata babbar hanyar jigilar kaso daya bisa biyar na man fetur na duniya da yawancin na kasarta bayan da Tehran ta rufe mashigar, ya gaza samun karbuwa. Kasar Saudiyya, ta jaddada bukatar warware rikicin ta hanyar diflomasiyya. Sai dai wasu manazarta na ganin cewa, sanarwar ta Abu Dhabi na da wata manufa ta dabam.

Ina makomar alakar Riyadh da Abu Dhabi?

Ko kafin rikicin rufe Mashigar Ruwan Hormuz, akwai tsamin dangantaka tsakanin Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa. Kasashen biyu, sun riga sun goyi bayan bangarorin da ke adawa da juna a Sudan da Libiya da Yemen. Duk da cewar sun ci gaba da kasancewa kawayen Amurka, Abu Dhabi ta sanya hannu kan yarjejeniyar daidaita al'amura da Isra'ila a shekarar 2020. Saudiyya a nata bangaren ta dakatar da irin wannan tattaunawar, bayan harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktoba 2023 da kuma yakin shekaru biyu da ya biyo baya a Gaza.

Fassara: Zainab Mohammed Abubakar

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW