1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya

Gaza: Mece ce makomar rayuwar yara?

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim LMJ
August 27, 2025

Gidauniyar Taimakon Kananan Yara ta Save the Children ta ce, mawuyacin halin da kananan yara ke ciki a Zirin Gaza na Falasdinu ya kai makurar da ko kuka ba sa iya yi saboda rashin kuzari.

Gaza | Khan Younis | 2025 | Yara | Mutuwa | Yaki | Yunwa | Agaji | Isra'ila
Kananan yaran Zirin Gaza na ci gaba da galabaita saboda yunwaHoto: Moaz Abu Taha/APA Images/ZUMA/picture alliance

Babban jami'in yada labarai na gidauniyar ta Save The Children Dan Stewart ne ya bayyana a lokacin da yake tattaunawa da tashar DW a Zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da dakarun sojan Isra'ila ke ci gaba da yi wa yankin luguden wutar bama-bamai a kokarin da suke na mallake yankin baki-daya. Bugu da kari gidauniyar ta Save The Children ta koka da karancin kayan agaji da take fuskanta tsawon watanni, inda manyan motocinta 45 makare da kaya ke makale a kan iyaka sanadiyyar tarnakin da Isra'ilan ta yi wa duk wani yunkurin isar da su Gaza.

A wannan gaba da Isra'ila ke zafafa hare-hare a Gaza, kasashen duniya na ci gaba da kiraye-kirayen ganin ta mayar da wukarta cikin kube albarkacin rayukan jama'a da ake ci gaba da rasawa ba dare ba rana. Jamus na cikin irin wadannan kasashe da ke wannan jan hakali, inda ministan harkokin wajenta Johann Wadephul ya ce kare rayukan fararen hula na zama babban muradin da Jamus ta sa a gaba. A cewarsa wannan mamaya da Isra'ila ke matsa lamba a kokarinta naa aiwatar da ita ba za ta haifar da alheri ba, face kara haddasa asarar rayukan jama'a. Yanzu haka dai al'ummar Gaza na tserewa daga yankin, domin kaucewa zafafan hare-haren Isra'ilan.