Nijar: Ina makomar sojojin da suka yi bore?
September 3, 2026
Babban hafsan sojojin Nijar din ya yi kira tare da cewa, za a yi maraba da duk sojan da ya kai kansa cikin ladabi da biyayya a makarantar horon jandarmomi da ke Yamai. Sannan an yi kira ga al'umma da ta bayar da hadin kai duk sanda taga irin wadannan sojoji, domin ganin an samu karbar dukkanin makaman da aka fito da su daga barikokin sojojin.
Kiyaye dokokin aikin soja
Cikin wata sanarwa babban hafsan hafsoshin kasar ta Nijar Janar Salau Barmou ya sakawa hannu ne ake kira ga sojojin da suka yi bore, musamman wadanda suka gudu akasari dauke da nasu makaman. Sanarwa ta ce, ta haka ne za a kiyaye tsarin dokar aikin soja yadda yake a cikin rundunonin sojojin kasar na FAN da nufin ganin an koma cikin ta farkin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Gamayyar kungiyoyin fararen hula sun gudanar da wani taron gangami da mambobin gwamnati da ma shugaban majalisar mashawarta suka halarta, domin nuna goyon baya ga zaman lafiya da hadin kan 'yan kasa da yin tir da matakin boren sojojin. Ismael Mohamed na kungiyar Niger Debout masu rajin kishin kasa da hadin kai, ya yi kira ga sojojin da su san nauyin da ke kansu su amsa kiran babban hafsan sojojin na kasa. Mayar da makamai na kasa ya zama wajibi, a cewar masana harkokin tsaro.
Za a yi adalci ga kowa
Duk da cewa an yi wa dokokin aikin soja karan tsaye wajen kai wa muradan kasa farmaki tare da haddasa barna mai yawa, hakan ba yana nufin shari'a ba za ta yi adalci ga wasu ba matukar suna da hujja a cewar Alkassoum Abdourahamane mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Sahel. Tun dai lokacin da aka soma wannan karon batta tsakanin sojoji masu bore da sojojin da ke biyayya ga gwamnati, mutane da dama sun sanar da ganin kakin soji a zube. Hakan na nuni da cewa, wasu sojojin sun cire kayan da ke jikinsu sun ranta a na kare.