1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAustraliya

Australia: Mece ce makomar 'yan ci-rani

September 8, 2026

Kwaskwarimar da Austiralia ke yi a sashen kula da shige da ficen kasar, ya fara tasiri kan yawan ma'aikata musamman a jami'o'i da ma yanayin tattalin arziki.

Australia | Dokoki | Shige da Fice | Anthony Albanese
Firaministan Australia Anthony AlbaneseHoto: Mick Tsikas/AAP/REUTERS

Austiralia ta ce, ta dauki wannan matakin ne ganin yadda shigar baki kasar ke yin tasirin wajen daidaita tsakanin yawan al'umma da tanadin da kasa ta yi na ababen more rayuwa. A karkashin sabon tsarin da ake kokarin aiwatarwa, za a mayar da hankali a kan ma'aikatan da ke karbar albashi mai toska wajen bayar da takardun izinin shiga kasa wato visa. Haka nan ma, shirin zai mayar da hankali a kan wadanda ke aiki a muhimman fannoni kamar kiwon lafiya da manyan gine-gine da fasaha.

Mece ce makomar ma'aikata 'yan ci-rani?

Masu fashin baki da masana tattalin arziki sun ce, wannan matakin na da dadari kasancewar bai yi la'akari da masana'antu kamar na noma da kiwo da ma masu aikin otel da yawanci ke dogaro da 'yan ci-rani musamman a lokacin bazara da ake samun yawan masu yawon bude idanu. Sai dai ministar kula da harkokin cikin gida Clare O'Neil ta kare matakin da cewa, kasar na gina tsarin shige da fice ne wanda ke la'akari da abin da zai fi amfanar Australia ba kara yawan adadi kadai ba. Shi ma ministan ilimi Jason Clare ya goyi bayan daukar kwararru ko da kuwa a matakin jami'a ne, domin kasar za ta more su ko da na wani tsawon lokaci ne kafin su koma gida.

Baki da dama na zuwa karatu AustraliaHoto: AAP/IMAGO

Sai dai jami'o'in kasar na gargadin cewa, yin hakan za iyi tasiri kan yawan daliban da aka saba dauka musamman a yankunan karkara saboda yawancin jami'o'in da ke wurin na dogaro ne da daliban da ke zuwa daga kasashen ketare, kuma ba lallai ne a karantar da abubuwa kamar aikin likitan a karkara ba. 'Yan adawa sun goyi bayan jami'o'in, inda suke fadin yawanci wadanda kan zo karatu suna karanta abin da suka san idan sun kammala za a dauke su aiki. A cewarsu in har aka ce sai likitoci da masana fasaha wadanda ke zuwa su yi aiki a fannonin da aka fi bukatar ma'aikata a karkara ba za su iya zuwa ba ke nan, kamar yadda Bridget Mckenzie 'yar adawar da ke kula da harkar gine-gine da tsare-tsare a majalisa ta bayyana.

Ya makomar Autralia za ta kasance?

Masana tattalin arziki sun ce, wannan sauyin zai tantance irin wadanda za su iya shiga Australia da kuma masa'na'antun da za su fi jin jiki. Baki su ne ginshikin masana'antu kamar gidajen kula da tsofaffi da noma da kiwo da shakatawa da a yanzu haka tuni sun fara fama da karancin ma'aikata. Yayin da Australia ke kokarin tantancewa da ma sake ma'anar abin da take nufi da kwararre ko kwararriya a  kan daukar baki aiki, shekaru 10 masu zuwa za su tantance irin mutanen da za su kasance masu hali a kasar da za su iya gina gidan kansu su koyar da dalibai su kuma kula da  tsofaffi – wato ainihin bakin da za su tabbatar da kyakkyawar makoma mai dorewa.

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Adam

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW