1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTanzaniya

Tanzaniya: Zargin musgunawa 'yan adawa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim LMJ
May 19, 2025

Jagoran adawar Tanzaniya Tundu Lissu da ke fuskantar hukunci ya gurfana gaban kotun kasar bisa tuhumar cin amanar kasa, inda cincirundon magoya bayansa suka rinka yi masa tafi suna yi masa jinjina.

Tanzaniya | Jagoran Adawa |  Tundu Lissu
Jagoran adawar Tanzaniya, kana tsohon dan takarar shugaban kasa Tundu LissuHoto: Emmanuel Herman/File Photo/REUTERS

Babban laifin da Jagoran adawar Tanzaniya Tundu Lissu ya aikata shi ne kiran a yi wa dokokin zaben kasar garanbawul, domin tabbatar da gaskiya da adalci. An kama Mr. Lissu ne a ranar tara ga watan Afirilun da ya gabata, a daidai lokacin da yake tsaka da jawabin yakin neman zabe yana mai kambama manufarsu da cewa matukar ba a yi wa dokokin zabe kwaskwarima ba to ba za su shiga zaben ba. Ya kuma halarci zaman kotun ne, sanye da riga mai dauke da wannan rubutu na babu gyaran kundin zabe to babu zabe. 

Karin Bayani: 'Yan adawa sun zargi gwamnatin Tanzaniya da kama karya

A zamansa na kurkuku jagoran jam'iyyar Chadema ya shiga yajin cin abinci, domin nuna kin amincewarsa da halartar shari'a ta boye aai dai wadda za a yi masa a sarari a gaban jama'a. Mr. Lissu ya umarci magoya bayansa da su kasance cikin karsashi da kwarin gwiwa, a wannan lokaci da suke fuskantar jarrabawa. Masu gabatar da akrar sun nemi kotun ta ba su karin makonni biyu da za su ba su damar kara fadada bincike kafin ci gaba da shari'ar, inda kotun ta tsayar da ranar daya ga watan Yuni mai kamawa domin ci gaba da sauraron shari'ar.

Shugaba Samia Suluhu Hassan ta TanzaniyaHoto: State House of Tanzania

Gabanin fara sauraron wannan shari'a sai da hukumomin Tanzaniya suka cafke fitacciyar 'yar adawar kasar Kenya kuma tsohuwar ministar shari'a Martha Karua da ta taba yin takarar shugabancin kasar a filin jirgin sama na Dar es Salaam tare da mayar da ita kasarta, bayan da ta je Tanzania da nufin halartar shari'ar Lissu da kuma karfafa masa gwiwa. Karua dai, ta taba zama lauyar jagoran adawar Yuganda Kizza Besigye har ma ta kare shi a kotu. Haka zalika an kama tsohon alkalin-alkalai na Kenya Willy Mutunga a filin jirgin saman birnin Dar es Salaam tare da wasu 'yan gwagwarmayar kasar da suka je, domin mara wa Lissu baya.

Karin Bayani: An saki jagoran adawar Tanzaniya, Freeman Mbowe

Ko da yake, sakataren ma'aikatar harkokin wajen Kenya Korir Sing'oei ya bukci mahukuntan Tanzaniyan su saki mutanen. Hukumomi da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na cikin gida da waje, sun zargi Shugaba Samia Suluhu Hassan ta Tanzaniya da muzgunawa 'yan kasartamusamman ma 'yan adawa. To sai dai, gwamnati ta sha musanta wannan zargin. Jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi wato CCM ta Suluhu Hassan ce dai ke mulkin Tanzaniya, tun bayan samun 'yancin kan kasar a shekara ta 1961.