Mene ne fa'idar ganawar Tiani da tsaffin shugabannin kasa?
June 17, 2025
A hakumance, gwamnatin Nijar ba ta tabbatar da faruwar ganawa ta musamman da shugaban kasa Janar Abdourahamane Tiani ya yi da tsaffin shugabannin kasa da tsaffin shugabannin gwamnatocin Nijar ba, ko kuma batutuwan da suka tattauna a wannan haduwarsu ba. Amma, wasu majiyoyin masu karfi sun tabbatar da faruwar haduwar wacce ke zama ta farko da Shugaban Tiani ya yi da wadannan 'yan siyasa tun bayan juyin mulkikusan shekaru biyu da suka gabata.
Honnorable Gousmane Abdourahamane, wani tsohon dan majalisar dokoki a Nijar ,ya ce ko da yake ganawar ta zo da latti, amma ba ta baci ba.
Karin bayani: Kungiyoyin kasa da kasa na neman a saki Bazoum
Ganawar da shugaban kasa ya yi da tsaffin magabatan kasar Nijar na zuwa ne kusan watanni hudu bayan matakin soke jam’iyyun siyasar kasar a bisa shawarar babban taron mahawara na kasa. Kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da kasar Nijar ke ci gaba da fuskantar kalubale ciki har da na tsaro.
Sai dai Soule Oumara, na kungiyar FCR na ganin soma tattauanawa da 'yan siyasa zai iya yin tasirin wajen shawo kan matsalolin da kasar Nijar ke fuskanta.
Sabanin ra'ayin kan ganawar Tiani da tsaffin shugabanni
Sai dai, a daidai loakcin da wasu ‘yan Nijar ke yabawa da matakin shugaban mulkin soja Janar Tiani na ganawa da tsaffin shugabannin kasar, wasu 'yan Nijar na ganin matakin a matsayin wani babban kuskure da ka iya mayar da hannun agogo baya ga tafiyar samar da sabuwar Nijar da ake kai tun bayan juyin mulki. Malam Abdourahmane Ide, shugaban wata kungiyar matasa a Nijar na daga cikin masu irin wannan ra’ayi.
Karin bayani: Rikici ya ki cinyewa tsakanin Talon da Janar Tiani
Ko shugaban kasar Nijar Janar Tianizai ci gaba da irin wanann ganawa da tsaffin ma’ikantan kasar da ma yin ta a bayyane kamar yadda wasu 'yan kasar suka bukata, ko kuma zai noke ne kamar yadda wasu 'yan Nijar ke fatan ganin ya ci gaba da mulki har sai ya saita Nijar kamar yadda suka bukata?