Menene ma’anar Jan digon goshin Matan Indiyawa
August 28, 2007Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.
Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Murjanatu Salihu Yar-Najeriya mazauniya a kasar Saudiyya, kuma mai sha’awar al’adun Indiyawa. Malamin yana tambaya ne akan cewar; Shin ko menene dalilin da ya sa Matan indiyawa suke yin Jan digo a goshinsu? Da me ake yin sa, kuma suna da shekaru nawa suke fara yi?
Amsa: To takaitacciyar amsa dai game da wannan batu shine cewar; Wannan Jan digo da Matan Indiyawa suke yi a goshinsu suna kiransa da suna “Tika’’ Idan kuma digon zagayayye ne to suna ce masa “Bindi’’ Kuma wannan wata alama ce dake nuna cewar matar da take da wannan digo a goshonta Matar aure ce.
A da ana yin wannan Jan digo na al’ada wato (“Tika’’ a indiyance) da wasu sunadarai na musamman, wanda a cikinsu harda toka, da kuma abin yin turaren wutar nan da ake kira “Sandalwood’’ amma a yanzu saboda sauyin zamani ana yin sa ne da wani ruwa na musamman ko kuma ayi hodarsa ta musamman, kai a wani lokaci ma ana yin sa da daye-manna wato (Sticker) a turance.
To sai dai a halin yanzu saboda sauyin zamani, Matan na indiya basa bin wannan al’ada sosai kamar da, kuma ma dai a yanzu amfi daukar yin wannan digo na goshi a matsayin kwalliya mai makon al’ada da aka gada iyaye da kakanni.